Crystal Palace ta yi wa Liverpool bace da ci 2-1

Benteke ya ci Liverpool kwallo biyar kenan Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Christian Benteke ya zamar wa Jurgen Klopp raina-kama-ka-ga-gayya

Christian Benteke ya zamar wa tsohuwar kungiyarsa dan-hakin-da-ka-raina, a wasan da Crystal Palace ta ziyarci Liverpool ta doke ta 2-1, inda ta kara damarta ta tsira, tare da dagula lissafin Jurgen Klopp na karewa cikin kungiyoyi hudu na gaba a Premier.

Benteke ya ci kwallo dai-dai kafin a tafi hutun rabin lokaci da kuma bayan an dawo, a minti na 42 da kuma na 74, bayan da suka yunkuro daga baya, bayan da Liverpool din ta fara zura musu kwallo a minti na 24 ta hannun Philippe Coutinho.

A bazarar da ta wuce ne Liverpool ta sayar wa Crystal Palace Benteke a kan fan miliyan biyar 5, kasa da yadda ta siyo dan wasan na Belgium a shekara daya kafin nan.

Palace wadda daman ta doke jagorar Premier, Chelsea ranar 1 ga watan Afrilu, a yanzu ta ci wasanninta shida daga cikin takwas na baya-bayan nan.

Ta hada maki 38, bakwai kenan tsakaninta da rukunin faduwa daga gasar, a matsayi ta 12, a wasa 33, abin da ke tabbatar mata damar sake buga gasar a kaka ta gaba.

Haka kuma nasarar ta gidan Liverpool wadda ta zama ta uku a jere, ta sa ta zama kungiya ta farko bayan Chelsea wadda ta yi hakan a watan Oktoba na 2005.

Yanzu Liverpool tana matsayi na uku da maki 66 a wasa 34, a gaban Manchester City ta hudu mai maki 64 amma a wasa 32, da kuma Manchester United ta biyar mai maki 63, ita ma a wasa 32.