Tasirin nasarar Barcelona kan Real Madrid

Messi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lionel Messi ya sha kwallonsa na 31st a gasar La Liga na kakar bana

Lionel Messi ya ci wa Barcelona kwallonsa ta 500, abin da ya sa kungiyar ta hau saman teburin gasar La Liga a nasarar da ta zo dab da a tashi a wasan.

Barca, wadda nasararta ta tura ta saman teburi saboda ta fi Madrid yawan kwallo, tana da sauran wasanni biyar, yayin da Real take da wasanni shida.

Casemiro ne ya ci wa masu karbar bakuncin wasan kwallon farko kafin Messi da Ivan Rakitic su sa Barcelona ta tsere wa Madrid inda daga bisani aka ba wa Sergio Ramos jan kati.

Messi da Cristiano sun barar da damar shan kwallaye daga farko .

Real wadda ta fi Barcelona yawan wasannin da za ta buga - ta ji ya kamata a ba ta bugun fenareti a lokacin da Samuel Umtiti ya yi wa Ronaldo keta minti biyu da fara wasa.

Hakkin mallakar hoto BBC Hausa
Image caption Irin nasarar da kulob-kulob suka yi a karawarsu da juna shi ake amfani da shi wajen bambanta matsayinsu idan makinsu ya zo daya.

Shin Barca ta fice daga matsala?

Kaiwa matakin kusa da dab da na karshe da kuma yin gogayya wajen lashe gasar La Liga zai yi wuya su kasance matsala ga yawancin kungiyoyin kwallon kafa, amman wannan Barcelona ce.

Yawanci lashe gasa ne abu mafi karanci da ake nema daga duk wani koci da ke jan ragamar Camp Nou. Magoya baya sukan tsammaci cin wasa cikin kwarewa kuma a baya sun nuna rashin amincewa da kwarewar kociya Luis Enrique, wanda zai bar kungiyar a karshen kakar bana.

Amman magoya bayan, wadanda suke kan hanya ba za su iya bayani kan jaruntakar da kungiyarsu ta nuna ranar Lahadi ba. Duk da haka Messi ya kayatar da su da kwallaye biyu kuma kwallon da Rakitic ya zura ya gamsar da su.

Za a iya daga duk wata maganar matsala a lokacin da kungiyar ke cigaba da tinkaho da Messi inda hatsabibin dan wasan yake nuna cewar har yanzu zai iya taimaka wa Barca ta kara da kungiyoyin kwallon kafa da suka fi kwarewa a duniya.

Dan baiwar kwallon kafan, ya ci gaba da taka rawar gani a Barcelona har bayan da Casemiro ya yi masa keta.

Ladan da Messi ya samu bayan haskaka tauraronsa fiye da na Christiano Ronaldo, shi ne kara dasa sunansa a tarihin Barcelona.

Har yanzu Madrid ce za ta iya barar da gasar da kanta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Casemiro ne ya fara ci wa Real Madrid kwallo a minti na 28

Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai a kaka biyu cikin ukun da suka gabata, amman ba sa samun nasara a wasannin cikin gida. Ba su lashe gasar La Liga ba tun shekarar 2012 inda Barcelona ta lashe kofin sau uku kuma Atletico Madrid ta lashe sau daya.

Bayan an bai wa Ramos jan kati, kuma Madrid ta rama shan da Barca ta yi mata, kungiyar ta Zinedine Zidane ta yi kamar za ta sha kwallon da zai ba ta nasara.

Amman wannan ya bai wa bakin damar sha. Rashin kwarewa ne daga Zidane? Mai yiwuwa ne, amman tun da tana da sauran wasa daya a gasar fiye da sauran takwarorinta, da alama Real Madrid ce za ta iya barar da gasar da kanta.

Idan kungiyar Zidane, wadda ta kamo hanyar zama kungiya ta farko da za ta lashe gasar Zakarun Turai sau biyu a jere, za ta iya cin wasanninta shida da suka rage a La Liga, Zidane zai iya kawo karshen jiran lashe kofin cikin gidan wanda Real Madrid ta shafe shekara biyar tana yi.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sai wa kuma? Lionel Messi ya sa Barca ta yi nasara a wasan da kwallaye biyun da ya ci ta yadda ya yi wa Barcelona a lokaci da dama,

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba