Ba na tunanin ritaya - Ibrahimovic

Ibrahimovic, a lokacin da ya ji raunin a Old Trafford Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ibrahimovic, mai shekara 35, ya tunkaro karshen kwantiraginsa na shekara daya a Old Trafford

Dan wasan gaba na Manchester United Zlatan Ibrahimovic ya ce, ba ya tunanin barin wasa a yanzu, kuma zai dawo da karfinsa fiye da da, bayan da ya ji raunin da zai yi jinya ta tsawon lokaci, a guiwarsa.

Dan wasan mai shekara 35 ya ji raunin ne a kusa da karshen minti 90 na wasan da suka yi na dab da kusa da karshe na Europa, na zagaye na biyu da Anderlecht, a makon da ya gabata.

Ibrahimovic shi ne kan gaba wajen ci wa United kwallo a bana, inda ya ci mata kwallo 28, amma yanzu ba a san lokacin da zai dawo wasa ba.

Dan wasan dan Sweden ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa, "zan yi jinya ta wani lokaci, amma ba maganar barin wasa a yanzu."

Ya kara da cewa, ''a yanzu ina wasa da kafa daya, amma ba wata matsala ba ce wannan.''

Ibrahimovic ya koma Manchester United ne bayan da kwantiraginsa da Paris St-Germain ta kare a kakar da ta wuce, amma har yanzu bai amince da tsawaita kwantiraginsa na shekara daya ba da kungiyar.

Shi ma Marcos Rojo ya ji rauni a guiwarsa a wannan wasa da Ibrahimovic ya ji ciwon, inda ya yi karo da wani dan wasa, aka cire shi a minti na 23 da wasa.