Kante ya zama gwarzon bana a Ingila

N'Golo Kante da lambar yabon Hakkin mallakar hoto Others
Image caption N'Golo Kante ya doke Hazard da Kane da Lukaku da Ibrahimovic da Sanchez a zaben

Dan wasan tsakiya na Chelsea N'Golo Kante ya ci lambar yabo ta gwarzon dan wasan kungiyar kwararrun 'yan kwallon kafa ta Ingila ta kakar 2016-17.

Dan wasan na Faransa mai shekara 26, ya doke Eden Hazard da Harry Kane da Romelu Lukaku da Zlatan Ibrahimovic da kuma Alexis Sanchez, a zaben da takwarorinsa 'yan wasa suke kada kuri'a.

Dan wasan Tottenham Dele Alli a karo na biyu a jere ya samu lambar yabo ta kungiyar ta gwarzon matashin dan wasa.

'Yar wasan Manchester City Lucy Bronze ita ce ta ci lambar gwarzuwar 'yar wasa ta kungiyar a bana.

Yayin da Jess Carter ta Birmingham ta kasance gwarzuwar matashiyar 'yar wasa ta kakar.

Hakkin mallakar hoto N'Golo Kante
Image caption A watan Yuli ne N'Golo Kante ya koma Chelsea daga Leicester

Kante wanda ya yaba da zaben da 'yan wasan suka yi masa ya ce babbar karramawa ce a gare shi, amma ya ce, ta samu ne da hadin guiwar abokan wasansa.

Dan wasan na tsakiya na kan hanyar sake daukar Kofin Premier da Chelsea, bayan da a kakar da ta wuce ya dauka da Leicester.

Tsohon Kyaftin din Ingila David Beckham ya samu lambar yabo ta kungiyar kwararrun 'yan wasan na Ingila sabod irin gudummawar da ya bayar a wasan kwallon kafa, a yayin bikin ba da lambobin da aka yi a ranar Lahadi.

Kante ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar ban mamaki da Leicester ta yi ta daukar Premier a shekarar da ta wuce.

Kuma zai iya bajintar zama dan wasa na farko d ya dauki kofi a jere da kungiyoyi daban-daban, idan har Chelsea ta ci gaba da ba wa Tottenham tazara a bana.

Tun lokacin da Chelsea ta sayo Kante a watan Yuli, ta ci gaba daga matsayin da take na tsakiyar tebur zuwa sama, yayin da ya rage wasa shida a kammala gasar ta bana.

Dan wasan na Faransa ya taka leda a duk mintunan wasannin Premier na bana da kungiyarsa ta yi, in banda wasan da suka yi da Bournemouth, ranar 26 ga watan Disamba, a lokacin da aka dakatar da shi sakmakon katin gargadi da aka ba shi a wasansu da Crystal Palace, da kuma mintuna 11 da suka yi da Tottenham ranar 4 ga watan Janairu.