Kun san dan wasan da ya fi Messi da Ronaldo?

Adama Traore na Middlesbrough da Spaniya Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Adama Traore ne gwarzon dan wasa na daya a Turai.... idan ana maganar iya yanka a wasa ne

A fagen wasan kwallon kafa wata tambaya da aka dade ana yi a wannan zamani ita ce - wane ne ya fi? Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo?

To yanzu dai ta tabbata akwai wani dan wasa da ya fi su duka biyun, dan wasan kuwa ba wani ba ne illa Adama Traore na Middlesbrough.

Kamar yadda wani nazari da Cibiyar Nazarin Harkokin Wasanni ta Duniya (International Centre for Sports Studies (CIES)), ta yi, dan wasan mai shekara 21 dan Spaniya shi ne ya fi kowa a Turai, idan ana maganar iya yanka ne a wasa.

Cibiyar ta samu wannan sakamako ne bayan da ta kasafta yawan yankan da kowane dan wasa yake samun nasara a duk lokacin da ya yi yunkurin yin hakan, da kuma wadanda ba ya samun nasara.

Daga nan ne Cibiyar ta fito da sunayen 'yan wasa 100 da suka kware a yanka a manyan gasar kwallon kafa biyar na Turai.

A zaben Traore ya zama na daya a gaban Eden Hazard na Chelsea, yayin da Messi na Barcelona ya zamo na shida, a bayan dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha.

Dan wasan gaba na Barcelona Neymar shi ne na hudu, a binciken, wanda Cristiano Ronaldo ko ambato shi ma ba a yi ba a gwanayen 'yan wasan 100 da suka iya yanka a wasan na tamola.

To sai dai kuma gwanintar yankan ta Traore ba ta yi wani tasiri ba sosai ga kungiyar ta Middlesbrough, domin ba wta kwallo da ya ci mata, in banda daya kawai da ya bayar aka ci, yayin da kungiyar ke zaman ta biyun karshe a teburin Premier.