Zan so mu yi wasanmu da Man Untd ba tare da lafari ba - Toure

'Yan wasan Man City Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Doke City da Arsenal ta yi na nufin a karon farko Pep Guardiola zai kare kakar wasa ba tare da kofi ko daya ba a aikinsa na kociya

Yaya Toure ya ce zai fi so su yi wasansu na hamayya na ranar Alhamis da Man United ba tare da alkalin wasa ba, bayan da ya soki alkalancin wasan da aka yi musu a lokacin da Arsenal ta fitar da Man City a Kofin FA.

A wasan da suka yi na kusa da karshe na Kofin na FA, alkalin wasa Craig Pawson ya hana kwallon da Sergio Aguero ya ci a kashin farko na wasan a Wembley, bisa dalilin cewa kwallon ta yi waje tun da farko kafin Aguero ya same ta.

Hotunan bidiyo da aka maimaita na wurin sun nuna ya kamata a ce alkalin wasa ya amince da kwallon a wasan da aka fitar da City da ci 2-1, bayan karin lokacin fitar da gwani.

Toure ya ce, abin ya ba shi takaici, yana ganin ya kamata alkalan wasa su daina haka, domin ba wannan ba ne na farko, akwai wasu lokutan da aka yi musu hakan.

Dan wasan ya ce, watakila ranar Alhamis za su samu alkalin wasan da ya fi kyau, ya kara da shaguben cewa ko ma dai su yi wasan ba tare da wani alkalin wasa ba, domin zai fi son ganin hakan.

Yanzu dai Manchester City ta mayar da hankalinta ga gasar Premier inda take ta hudu, amma United za ta yi mata tsallen-badake ta haure ta idan ta doke ta ranar Alhamis.