'Man Utd na da niyyar sayen Antoine Griezmann'

Antoine Griezmann Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Griezmann ya koma Atletico ne a watan Yulin 2014 a kan kudin da aka ce fan miliyan 24 ne

Wakilin dan kwallon Atletico Madrid Antoine Griezmann, ya ce Manchester United ce ta fi nuna sha'awar sayen dan wasan a duk cikin kungiyoyin da ke zawarcinsa.

Eric Olhats ya shaida wa wani shirin gidan talbijin na Telefoot a Faransa cewa United sun tattauna yiwuwar biyan farashin yuro miliyan 100 din da aka sanya wa dan wasan.

"United ce ta fara zuwa domin tattaunawa da mu kuma su ne suka fi nuna bukata sosai," a cewar Olhats.

Griezmann, mai shekara 26, ya zura kwallaye 25 a wasa 46 da ya buga wa Atletico a bana.

Mutumin da ya fi ci wa United kwallo a bana Zlatan Ibrahimovic ya zura 28 ne, sai dai shekararsa 35.

Kuma har yanzu bai cimma yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa ba wacce za ta kare a karshen kakar bana.

Ga shi kuma ya ji rauni wanda zai dauki lokaci kafin ya warke.

Ana sa ran Manchester City za ta bayyana nata tayin a wani kokari na saye dan kwallon na ksar Faransa.

Olhats ya kuma nuna cewa akwai wasu kulob din Turai da ke yunkurin sayen dan wasan wanda tauraruwarsa ke kara haskaka wa.

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba