Arsene Wenger na shirin sayen sabbin 'yan wasa

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsene Wenger na fuskantar matsin lamba daga wasu magoya baya kan ya bar kungiyar

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce yana shirin sayen sabbin 'yan kwallo domin tunkarar kakar wasa ta badi duk da cewa babu tabbas ko zai ci gaba da zama a kulob din.

A karshen bana ne kwantiragin Wenger za ta kare, kuma an ba shi damar sabunta ta na tsawon shekara biyu, amma har yanzu bai bayyana cewa zai karba ba ko kuma a'a.

"Zan ci gaba da aiki har ranar karshe ta kwantiragina," a cewar kocin mai shekara 67.

"Sayen 'yan wasa shi ne makomar kulob din kuma abu ne mai muhimmanci."

Ya kara da cewa makomata ba ita ce almuhimmu ba, abu mafi muhimmanci shi ne makomar kulob din."

A watan Fabrairu Wenger ya ce zai yanke hukunci kan sabon kwantiragin a watan Maris ko Afrilu kafin daga bisani ya ce "Na son abin da zan yi kuma kwanan nan za ku ji".

Har yanzu babu wata sanarwa da aka bayar, kuma Arsenal na kokarin samun gurbin shiga gasar zakarun Turai a badi - bata taba rasa wannan damar ba a shekara 21 da Wenger ya yi a kulob din.

A yanzu dai sun kai wasan karshe a gasar cin kofin FA bayan da suka doke Manchester City a Wembley ranar Lahadi.

Labarai masu alaka