An tuhumi Moyes da barazanar marin wakiliyar BBC

David Moyes, kociyan Sunderland Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kocin Sunderland David Moyes ya ce ya yi nadamar kalamansa ga wakiliyar BBC Vicki Sparks

Hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila, FA, ta tuhumi kocin Sunderland David Moyes bayan da shaida wa wakiliyar BBC Vicki Sparks cewa za ta iya "shan mari".

An nadi muryarsa a kyamara yana yin kalaman bayan da kulob dinsa ya yi canjaras da Burnley a gasar Premier.

Moyes ya bayyana matukar "takaicinsa" kan kalaman da ya yi.

Hakan ya biyo bayan tambayar da Vicki ta yi masa kan cewa ko zuwan da Ellis Short ya yi, mai kulob din, ya kara sa shi cikin tsaka-mai-wuya?

Moyes ya amsa mata da a'a, amma kuma bayan sun kammala hirar tasu, sai ya ce da ita gara ta rika yi a hankali, ta bar ganin ita mace ce, don wataran za ta sha mari.

Tsohon kocin na Everton da Manchester United dai ya bai wa Misis Sparks hakuri daga baya, inda ya ce ya yi matukar da-na-sanin fadar wadannan kalaman.

Labarai masu alaka