Caca: An dakatar da Joey Barton na Burnley

Joey Barton na Burnley da Scotland Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An taba dakatar da Joey Barton wasa daya a watan Nuwamba a kan caca

An dakatar da dan wasan tsakiya na Burnley, Joey Barton, daga wasa na tsawon wata 18 bayan da ya amsa tuhumar da aka yi masa ta laifin da yake da alaka da caca.

An ci tarar dan wasan mai shekara 34, kudi fam 30,000, an kuma gargade shi da kada ya aikata irin wannan laifi a gaba, bayan da aka tuhume shi da laifin karya dokar FA na yin caca har sau 1,260 a wasanni tsakanin 26 ga watan Maris na 2006 da 13 ga watan Maris din 2016.

Barton na shirin daukaka kara kan tsawon lokacin da aka dakatar da shi, yana mai cewa ; "wannan mataki zai tilastamin yin ritaya da wuri".

Dan wasan ya yi caca a kan wasu wasannin da ya buga, sai dai ya fada a wata sanarwa a shafinsa na intanet cewa, "wannan ba cogen wasa ba ne, kuma ba wani lokaci da aka ga wani abu na rashin gaskiya a game da ni yayin wasannin".

Ya kara da cewa: "Na yadda na karya dokar kwararrun 'yan wasa, amma ina jin hukuncin ya yi tsauri, fiye da yadda za a yi wa 'yan wasan da suka yi abin da bai kai wannan ba''.

Labarai masu alaka