Ana binciken Newcastle da West Ham kan zamba

Tambarin kungiyoyin Newcastle da West Ham Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana zargin jami'an kungiyoyin biyu da kin biyan harajin kusan fan miliyan biyar

Jami'an haraji sun yi wa filayen wasan Newcastle United da West Ham United dirar mikiya kan zargin zamba ta kin biyan haraji.

Ana ganin babban daraktan kungiyar Newcastle Lee Charnley na daga cikin tarin mutanen da aka kama wadanda ke cikin harkar kwallon kafar kwararru.

Hukumar da ke kamen (HMRC) ta ce ta baza jami'ai 180 a fadin Birtaniya da Faransa don gudanar da aikin sumamen.

BBC ta fahimci cewa yawan kudin harajin da ya kamata kungiyoyin biyu su biya amma suka ki biya ya kai fan miliyan biyar.

Jami'an sun binciki ofisoshin kungiyoyin da ke filayensu a yankin arewa maso gabas da kudu maso gabashin Ingila, inda suka kwace muhimman takardun bayanan kudi da kwamfutoci da wayoyin salula.

Jami'an sun fadada binciken nasu har zuwa ofisoshin kungiyar Chelsea, kamar yadda mai Magana da yawun kungiyar ya tabbatar.

Sai dai ana ganin ba sumame aka kai ofisoshin ba kuma ba a kama kowa ba a can, illa dai jami'an sun bukaci wasu bayanai ne game da kungiyar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lee Charnley ( daga dama tare da mai kungiyar Newcastle Mike Ashley), na daga wadanda aka kama

Wasu majiyoyi sun sheda wa BBC cewa tun da farko sai da aka kama manajan daraktan Newcastle Mr Charnley, mai shekara 39.

Shekara uku da ta wuce ne manajan ya kama aikin, kuma ana ganin shi ne ya shawo kan kociyan kungiyar Rafael Benitez ya tsaya byan da ta fadi daga gasar Premier a bara.

A ranar Litinin ne kungiyar ta yi nasarar dawowa gasar ta Premier kwanaki 348 bayan da ta fadi.