An dakatar da Neil Taylor sabodo jikkata Coleman

Lokacin da alkalin wasa Nicola Rizzoli ya kori Neil Taylor Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alkalin wasa Nicola Rizzoli ya ba wa Neil Taylor jan kati bayan ketar da ya yi wa Seamus Coleman

An dakatar da dan wasan baya na Wales Neil Taylor, wasa biyu kan muguwar ketar da ya yi wa kyaftin din Ireland ta Arewa Seamus Coleman.

Alkalin wasa ya kori Taylor, mai shekara 28, saboda wannan keta da ya yi a lokacin wasan na neman gurbin gasar Kofin Duniya tsakanin Wales da Ireland ta Arewa a Dublin a watan Maris.

Yanzu dai dan wasan ba zai buga wasan da Wales za ta yin a neman damar zuwa gasar ta Kofin Duniya, guda biyu ba, da Serbia a watan Yuni da kuma Austria a watan Satumba.

Sakamakon raunin da dan wasan bayan na Everton, Coleman, ya ji ana ganin zai dade bai dawo tamola ba saboda tiyatar da aka yi masa a kauri.

Kociyan Everton Ronald Koeman, mai shekara 28, da kuma kyaftin dinsu, Phil Jagielka sun ziyrci dan wasan a gidansa a Ireland ta Arewa.

Ireland din it ace ta biyu a rukuninsu na hudu ( Group D), da maki daidai da Serbia wadda ke jagorantar rukunin, kuma tana da maki hudu a gaban Wales ta uku.