Kun san tasirin wasan hamayyar Manchester na Alhamis?

Guardiola da Mourinho Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Wasan na neman kasancewa cikin kungiyoyin hudun farko ne a Premier

An yi tsammanin kakar wasan Premier ta bana za ta zama gogayya ce tsakanin Guardiola da Mourinho,wajen daukar kofin Premier, sai dai hakan ba tabbata ba.

A ranar Alhamis ne za su kara karawa a filin wasa na Etihad, yayin da Guardiola ke fatan maimaita nasarar da ya yi, kan Mourinho a watan Satumba.

Waccan nasarar ta sanya City a saman teburin Premier, kuma tun daga wancan lokacin har yanzu babu wata kungiya ta Manchester da ta kara samun wannan damar.

Rabon da Manchester United dai, ta zama a saman teburin Premier, tun ranar 19 ga watan Agusta. Yayin da rabonta da zama cikin kungiyoyi hudun farko tun ranar 15 ga watan Satumba.

Yanzu dai yakin na neman kasancewa cikin kungiyoyi hudun farko ne, ba daukar kofi ba. Saboda samun gurbin shiga gasar Zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.

A rashin uwa akan yi uwar daki, ko kuma a ce da babu gara ba dadi, domin rashin daukar kofi ba shi ne abin damuwa a wajen Guardiola, kamar yadda ya ce, amma samun karewa cikin hudun farko shi ne burinsa a yanzu.

Samun nasarar zuwa gasar Zakarun Turai dai, shi ne zai fayyace matsayin Guardiola da Mourinho, a kakarsu ta farko a kungiyoyin nasu.

Idan dai United ta yi nasara a wasan na ranar Alhamis, za ta dawo cikin kungiyoyi hudun farko, a karo na farko tun 15 ga watan Satumba, kuma City za ta fice daga hudun farko, a karon farko tun ranar 12 ga watan Fabrairu.

Wasan na ranar Alhamis ba shi ne siradin karshe na samun gurbi a wasan Zakarun Turai ba, saboda duk kungiyoyin biyu na da sauran wasa biyar.

Kuma akwai sauran kungiyoyi biyu cikin wannan fafatawar, watau Liverpool da Arsenal wacce yanzu ta farfado.