Premier: Arsenal ta doke Leicester 1-0

Monreal na murna Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Monreal na murnar cin da Arsenal ta yi bayan da ya sheka kwallon da ta doki kirjin Robert Huth ta shiga raga

Arsenal ta ci gaba da fafutukar komawa cikin kungiyoyi hudu na farko a teburin Premier bayan da doke Leicester 1-0, bayan da Robert Huth ya ci kansu a minti na 84.

Magoya bayan Arsenal din sun kusa yanke kauna da samun nasarara a wasan na Emirates kafin Nacho Monreal ya sheko wata kwallo wadda ta bugi kirjin dan bayan na Leicester, dan Jamus ta shiga raga, ana dab da tashi.

Yanzu dai maki uku ne tsakanin Arsenal ta shida a tebur wadda ke bayan Manchester United ta biyar, sannan kuma hudu tsakaninta da ta hudu a tebur Manchester City tun da sun yi yawan wasanni daya.

Amma akalla daya daga cikin kungiyoyin na Manchester za ta rasa maki idan sun hadu a wasansu na hamayya na ranar Alhamis.

Liverpool tana matsayi na uku da maki shida a gaban Arsenal, amma kuma ta fi Gunners din da yawan wasa biyu.

Wasan Sunderland da Middlesbrough:

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasa biyar Middlesbrough ta ci a kakar nan gaba daya

Sunderland ta ci gaba da zama kan siradin faduwa daga gasar Premier bayan da abokiyar fafutukarta ta tsira Middlesbrough ta doke ta 1-0, a nasararta ta farko a wannan shekara ta 2017.

de Roon ne ya ci wa Sunderland din wadda za ta hadu da Bournemouth ranar Asabar, kwallon a minti takwas da shiga fili.

Idan Sunderland din ba ta yi nasara ba a wasan za ta iya faduwa muddin sakamakon wasu daga cikin wasannin ba su yi mata kyau ba.

Ta biyun karshe Middlesbrough ba za ta fadi daga gasar ba a wasannin karshen makon nan, amma kuma suna fuskantar wasanni masu tsanani a nan gaba.

Za su hadu da Manchester City da Chelsea da Southampton da kuma Liverpool.Wasan Sunderland da Middlesbrough,