Tottenham ta ci gaba da matsa wa Chelsea, bayan ta ci Palace 1-0

Christian Eriksen lokacin da ya ci kwallo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Christian Eriksen ya ci kwallo biyar a wasa 12 da ya yi da suka gabata

Tottenham ta ci gaba da matsar jagorar Premier Chelsea mai maki 78, da tazarar maki hudu, bayan da ta je har gidan Crystal Palace ta doke ta da ci 1-0.

Bakin sun yi ta fama kan su samu damar keta masu masaukin nasu, amma abin ya gagara, sai a minti na 78 Eriksen ya samu ya daga ragar.

Palace wadda ta yi rashin jajircaccen dan wasanta na baya Mamadou Sakho saboda raunin da ya ji bayan an dawo hutun rabin lokaci, ba kasafai 'yan wasanta suke kai hari ba, sai dai hana bakin.

Yanzu Palace, ta ci gaba da zama ta 12 a teburin na Premier, da maki bakwai tsakaninta da rukunin masu faduwa daga gasar.