FA ta ce karamin hukunci ta yi wa Barton

Joey Barton Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barton ya soki hukumar kwallon kafa ta Ingila kan abin da ya ce dogaro da take yi da kamfanonin caca

Hukumar kwallon kafa ta ingila ta ce dakatarwar wata 18 da ta yi wa dan wasan Burnley Joey Barton, daga shiga duk wasu harkokin kwallon kafa, shi ne mafi karancin hukuncin da za ta yi masa, bayan da aka same shi da laifin caca.

A bayanan da hukumar ta gabatar a rubuce na dalilin da ta yi masa hukuncin a ranar Laraba, hukumar ta ce Barton ya yi caca sau 1,260 da ta kai ta fan 205,172, inda ya rasa fan 16,708.

Dan wasan na tsakiya na Burnley mai shekara 34 ya amince da saba dokokin hukumar wasan na shigar 'yan wasa caca, yana mai cewa caca ta zama jiki ne a wurinsa.

Hukumar ta FA ta lamunta da mawuyacin halin da dan wasan ya samu kansa ciki, musamman ganin cewa caca ta ratsa ko ina a wasanni.

Kuma ta ce ta yarda cewa Barton ba wai yana shiga cacar ba ne domin ya samu kudi, abin ta ce wannan shi ya rage girman laifin nasa.