Lovren zai ci gaba da zama a Liverpool

Dejan Lovren Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dejan Lovren ya buga wasa 28 a kakar wasa ta bana

Dan wasan Liverpool Dejan Lovren ya sanya hannu akan sabuwar kwantiragi wacce za ta bashi damar cigaba da zama a kulob din har zuwa shekara ta 2021.

Dan wasan mai shekara 27 ya koma Anfield ne daga Southampton a kan kudi fam miliyan 20 a shekarar 2014.

Lovren bai taka rawar gani a kakarsa ta farko ba, amma duk da haka ya buga wasa 105 inda ya zura kwallo hudu.

Dan kwallon na Crotia ya ce ''Ina ganin a yau ni ne mafi murna a duniya.''

Ya kara da cewa burina shi ne in dade a kulob daya da nake so kuma shi ne Liverpool.

Lovren ya buga wasa 28 a kakar bana.

Yana haskaka wa sosai a karkashin koci Jurgen Klopp kuma yana cikin 'yan wasan da ake ji da su, inda ake hada shi da Joel Matip domin tsare baya.

A lokacin da yake hira da shafin intanet na ya ce ''Bayan duk abin da ya faru a kaka biyu da ta gabata, ina ganin na fi kokari a kakar farko. Kulob din ya amince da ni, haka kuma magoya bayanmu.''

Labarai masu alaka