Canjaras ya ishe mu zuwa gasar Zakarun Turai - Antonio Conte

Antonio Conte Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ya ce daukar kofin Premier ne babban burinsa a yanzu.

Kocin Chelsea ya ce samun nasara ko yin canjaras a wasansu da Everton ranar Lahadi zai tabbatar musu da samun gurbi a wasan Zakarun Turai a kaka mai zuwa.

Ya kara da cewa "lokacin da muka fara wannan kakar wasa, burinmu shi ne samun gurbi a gasar Zakarun Turai mai zuwa."

"Wannan shi ne burin kungiyar, da magoya bayanta, da kuma 'yan wasan. Amma a yanzu muna matakin da muke fatan daukar kofin," in ji Antonio Conte.

Ya ce hakan "kyakkyawan ci gaba ne amma kuma daukar kofin Premier ne babban burinsa a yanzu."

Kocin na Chelsea ya kara da cewa a fili take cewa biyu daga cikin kungiyoyi shida tsakanin Chelsea, da Tottenham, da City, da Arsenal, da United, da kuma Liverpool, ba za su samu gurbi ba a gasar Zakarun Turai mai zuwa ba.

Yana wannan maganar ne, lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi kan wasansu na ranar Lahadi da Everton inda ya tabbatar da cewa duk 'yan wasansa sun shirya wa wasan.

Ya ce Everton kyakkyawar kungiya ce, kuma mai karfi, tana da manyan 'yan wasa a tawagarsu, kuma kungiya ce mai karfi.

Labarai masu alaka