Na dawo wa da Man Utd martaba da farin jininta - Mourinho

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mourinho ya zo Manchester United a watan Mayun 2016

Mourinho ya ce ya dawo wa da kungiyar farin jini, da martaba, da armashin da ta rasa a hannun tsohon kocinta Louis van Gaal.

Kocin ya ce sababbin 'yan wasa da za su zo kungiyar a kakar wasa mai zuwa "za su taimaka wajen samun manyan nasarori."

An kori Van Gaal ne a watan Mayun shekarar da ta gabata, bayan ya lashe kofin FA, amma kuma ya kasa kai kungiyar gasar Zakarun Turai.

A kakarsa ta farko a Old Trafford, Mourinho ya ci kofin kalubale, kuma ana sa ran zai kammala gasar Premier a matakin kungiyoyin hudun farko.

Ya kuma taimaka wa kungiyar kai wa wasan kusa da karshe a gasar Zakarun Turai ta Europa, inda za ta kara da Celta Vigo.

Ya ce "Ina tunanin Mista Van Gaal ya bar kyakkyawar kungiya, wadda 'yan wasanta ke da alaka mai kyau a tsakaninsu".

Sai dai sun rasa farin ciki, sun rasa karsashi, da martaba, amma wannan abin da suka samu yanzu zai taimaka wa kungiyar.

"Idan muka kara hada kungiyar ranar 19 ga watan Yuli kungiyar za ta zama mai karfi. idan sababbin 'yan wasan suka zo, kungiyar za ta shirya wa samun manyan nasarori", in ji Mourinho.

Wasan da kungiyar ta tashi canjaras ranar Alhamis tsakaninta da City, ya kara wa kungiyar yawan wasannin da ba a doke ta ba zuwa wasa 24.

Manchester United wacce yanzu ita ce ta biyar a kan tebur, da ratar maki daya tsakaninta da City, wacce ke mataki na hudu, wadda ita kuma ke bayan Liverpool da maki biyu tare da kwantan wasa daya. Za ta kara da Swansea ranar Lahadi mai zuwa.

Labarai masu alaka