Costa ne gwarzon ɗan wasan gaba na duniya - Conte

Diego Costa ya zura kwallo 19 a gasar Premier ta bana. Da ce bai zura su ba, da Chelsea ta rasa maki 15 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Diego Costa ya zura kwallo 19 a gasar Premier ta bana. Da ce bai zura su ba, da Chelsea ta rasa maki 15

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce Diego Costa shi ne ɗan wasan gaban da ya fi kowanne iya murza leda a duniya.

Chelsea, wacce ke kan gaba a gasar Premier za ta je gidan Everton ranar Lahadi, inda za su yi karon-batta da Romelu Lukaku, dan wasan da ya fi zura kwallo a gasar Premier ta bana.

Dan kasar ta Belgium, Lukaku, mai shekara 23, ya zura kwallo 24, yayin da shi kuma Costa, dan kasar Spain mai shekara 28, ya ci kwallo 19.

Conte ya ce, "Lukaku yaro ne mai gwaninta amma a wurinmu Diego yana da matukar muhimmanci, kuma shi ne ke share mana hawaye a bana."

"Muna magana a kan 'yan wasan gaba biyu mafiya iya taka leda. Amma, a wuria, Diego shi ne gwarzon dan wasan gaba a duniya," in ji Costa.

Kocin na Chelsea ya kara da cewa "Ina ganin yana da matukar basira. Amma abin da na fi ƙauna shi ne yadda dan wasan zai nuna shi gwarzo a lokacin da yake murza leda, fiye da haka kuma, idan 'yan wasa haziƙai suka nuna basirarsu ta yin aiki tuƙuru lokacin wasa."

Labarai masu alaka