Sakamakon wasan bana ya girgiza 'yan wasan Arsenal - Wenger

Wenger Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wenger ya ce 'yan wasansa sun kaɗu

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce wasu daga cikin sakamakon wasannin da aka yi a kakar wasa ta bana sun "girgiza" 'yan ƙwallonsa, sai dai ya dage cewa a shirye ƙungiyar take ta fafata da Tottenham ranar Lahadi.

Arsenal su ne na shida a teburin gasar Premier kuma suna bayan Manchester City, wacce ke mataki na huɗu, da maki shida ko da yake suna da sauran wasa shida da za su gwabza.

Wenger ya bayyana kashin da suka sha a hannun Bayern Munich da ci 5-1 a watan Fabrairu da kuma dokewar da Chelsea ta yi musu da ci 3-1 a matsayin "babban koma-baya."

Ya ce "Mun zama kawar wani ɗan dambe wanda aka kayar amma ya tashi sau biyu. Mun sha kashi amma mutane sun fassara hakan a matsayin abin da ba su damu da shi ba."

Kocin, mai shekara 67, ya kara da cewa "Watakila saboda sun damu sosai ne shi ya sa muka kaɗu sosai. Mun yi matukar kaɗuwa."

"Ina ganin 'yan wasan sun damu. Suna da kwazo. Ina son yadda suke nuna halayensu. Muna cikin yanayi mai kyau idan ka kwatanta da wata daya zuwa biyu da suka wuce," in ji Wenger.

A cikin wasanni 49 da Wenger, Arsenal ta yi nasara a 22, ta yi kunnen-doki a 20 sannan ta sha kaye a bakwai, amma ba ta doke Tottenham ko da sau daya ba a wasannin lig guda biyar da suka fafata.

Mauricio Pochettino shi ne kocin Tottenham na farko da ba a doke ba a gasa biyar da ya buga.

Labarai masu alaka