Swansea ta yi wa Man United fancale

Kwallon da Gylfi Sigurdsson ya ci wa Swansea a karawarsu da United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gylfi Sigurdsson ya ci wa Swansea kwallonsa ta farko tun watan Fabrairu

Swansea ta samu maki a fafutukar da take yi ta tsira a gasar Premier ba, yayin da kuma ta yi wa mai masaukinta Manchester United cikas kan neman shiga hudun farko da take yi, inda suka tashi 1-1.

Gylfi Sigurdsson ne da bugun tazara ya ci wa bakin kwallonsu a minti na 79, ya rama fanaretin da Wayne Rooney ya ci ana dab tafiya hutun rabin lokaci, wadda 'yan Swansea suka yi korafi da cewa Marcus Rashford faduwa ya yi da gangan, ba keta aka yi masa ba.

Sakamakon ya sa yanzu maki biyu ne tsakanin Hull City ta 17 mai maki 34, da Swansea ta 18.

Man United ta cigaba da zama ta biyar, da maki 65 maki daya tsakaninta da abokiyar hamayyarta Man City ta shida da maki 66, wadda da ta yi canjaras 2-2 da Middlesbrough yau Lahadi.

Bayan makin da United ta yi asara a gidan nata ta kuma gamu da matsalar rasa karin 'yan wasanta da suka ji rauni, inda a wannan karon ta rasa Eric Bailly da Luke Shaw, bayan daman 'yan bayanta Phil Jones da Chris Smalling da Marcos Rojo suna jinya.