Chelsea ta fara jin kanshin kofi bayan ta doke Everton 3-0

Conte da Cesar Azpilicueta Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Conte na murna da Cesar Azpilicueta bayan wasan, da ya kawo karshen karawarsu 11 ba tare da an ci su ba

Jagorar Premier Chelsea ta kara matsawa kusa da kofin sakamakon kwallo uku na bayan hutun rabin lokaci da ta zazzaga wa Everton a gidanta Goodison Park.

Chelsea ta yi jinkiri da kuma hakuri wajen neman kwallayen wadanda har sai da aka dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 66 Pedro ya daga ragar masu gidan.

Bayan minti 11 da fara cin sai Cahill shi ma ya zura tasa kafin Willian shi ma ya ci tasa a minti na 86, bayan wata kwallo da Fabregas ya sanya masa.

Nasarar ta sa Chelsea ta kara tazarar da ke tsakaninta da ta biyu Tottenham wadda za ta kara da Arsenal, ita ma a ranar Lahadin, da maki bakwai, inda yanzu take da maki 81 a wasa 34.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Pedro yana da hannu a kwallo hudu cikin takwas da Chelsea ta ci Everton a Premier bana

Hakan na nufin ko da Chelsea ta yi asarar maki uku a ragowar wasanninta hudu, za ta iya daukar kofin nata na biyu a shekara uku, ko da kuwa Tottenham ta ci dukkanin wasanninta.

Canjasar din da Manchester City ta yi a gidan Middlesbrough na nufin kungiyar ta Ronald Koeman (Everton), a matsayi na 7, tazarar maki 8 ne tsakaninta da rukunin hudun farko, yayin da ya rage wasa uku a gama gasar.

Wasan shi ne babban fatan Tottenham na ganin an ci Chelsea, domin Everton ce ake ganin tafi dukkanin sauran abokan karawarta hudu karfi, yayin da Chelsean za ta yi wasanni uku a gida.

Lissafin mai sauki ne ga Chelsea, domin yadda yake shi ne, idan ta ci karin wasa uku to shikenan za ta dauki kofin a karo na shida.

Kuma daga yadda kociyanta Conte da 'yan wasansa suka rika murna bayan wasan na Everton, kai ka ce sun ma riga sun dauki kofin, kamar sun gama da Middlesbrough da West Brom da Watford da kuma Sunderland.

Idan kuma har Chelsean ta yi nasara doke Arsenal a wasan karshe na Kofin FA, ranar 27 ga watan Mayu, za a ce Conte ya yi gagarumar nasara kenan a kakarsa ta farko a Ingila.