Tottenham ta ci gaba da matsar Chelsea da cin Arsenal 2-0

Harry Kane lokacin da yake buga fanaretin da suka ci Arsenal kwallonsu ta biyu Hakkin mallakar hoto PA
Image caption A duk haduwarsu da Arsenal biyar a jere a Premier Harry Kane sai ya ci Arsenal, wadda ya taso daga kungiyar matasan 'yan wasanta

Tottenham ta ci gaba da bin jagorar Premier Chelsea bayan da Dele Alli da Harry Kane suka zura kwallo biyu a ragar abokan hamayyarsu na arewacin Landan, Arsenal bayan hutun rabin lokaci.

Tottenham na bayan Chelsea da maki hudu yayin da ya rage wasa hudu a gama gasar, bayan da tun da farko Chelsean ta bi Everton gida ta doke ta 3-0.

Nasarar ta wasan na hamayya ta sa a karon farko tun kakar 1994-95 Tottenham za ta gama Premier a saman Arsenal.

Tun kafin tafiya hutun rabin lokaci masu masaukin bakin suka barar da damar kasancewa a gaba a wasan, inda Christian Eriksen da Dele Alli kowannensu ya barar da damar da ake ganin ruwa-ruwa za su ci.

Sai bayan da aka dawo daga hutun rabin lokacin ne a minti na 55 Alli ya ci kwallon wadda ita ce ta 21 da ya ciwa Tottenham a bana.

Dakika 146 tsakanin sai kuma Kane ya ci ta biyu da fanareti, bayan da Gabriel ya yi masa keta ya fadi a cikin da'irar Arsenal.

Kwallon da ta sa Kane ya zama kan gaba a 'yan wasan Tottenham da suka ci Arsenal, inda yake da shida, yayin da Gareth Bale, da ya koma Real Madrid, yake da biyar.

Arsenal mai kwantan wasa daya ta ci gaba da zama ta shida a tebur, maki shida tsakaninta da ta hudu Manchester City wadda take da maki 66.