Boksin: Fury ya amince da kalubalantarsa da Joshua ya yi

Tyson Fury Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tyson Fury ya ce yana son su dambata da Anthony Joshua, domin 'yan kallon da ba a taba samun yawansu ba, su kashe kwarkwatar idanunsu

Tyson Fury ya amsa kalubalantarsa da zakaran damben boksin na ajin masu nauyi na duniya Anthony Joshua na Birtaniya, dan asalin Najeriya, ya yi na su gwabza bayan doke Wladimir Klitschko da zakaran ya yi ranar Asabar.

Joshua, wanda ya gama da tsohon zakaran, dan Ukrain a turmi na 11 a filin wasa na Wembley, nan take ya kalubalanci Fury wanda shi ma dan Birtaniya, wanda shi ma ya doke Klitschko da yawan maki a karawar da suka yi a watan Nuwamba na 2015.

Bayan nasarar ta ranar Asabar ne, Joshua ya yi tambaya, ''Fury ina kake ne?" Ya ce: ''Na san yana ta magana, to ina son in ba wa 'yan kallo dubu 90 damar ganinmu."

Fury, wanda bai kara wani dambe ba tun lokacin da ya doke Klitschko, ya amsa kalubalantar da Joshua ya yi masa inda ya ce : "Ba ri mu taka rawa."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan shi ne karo na biyar da ake doke Wladimir Klitschko a sana'arsa ta damben boksin

Yanzu dai ba a taba doke Joshua a damben da ya yi 19 ba. Kuma nasarar da dan damben dan asalin Najeriya mai shekara 27 a gaban yawan 'yan kallo 90,000 da ba a taba samu ba a Birtaniya tun bayan yakin duniya a babban filin wasa na Wembley, ya kara hada kambin WBA a kan na IBF da yake rike da shi.

Shi ma Fury, mai shekara 28, ba a taba doke shi ba tun da ya fara damben boksin na kwararru, inda ya doke abokan karawarsa 18 a dambe 25.

Amma kuma ya saryar da kambinsa biyu na duniya, domin ya samu dama ya mayar da hankalinsa wajen maganin larurar kwakwalwa da ke damunsa, sannan a yanzu ba shi da lasisin yin dambe.