Wariyar launin fata: An ba wa Sulley Muntari katin gargadi kan korafi

Sulley Muntari yana ficewa daga fili Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sulley Muntari ya fice daga fili yana nuna wa magoya bayan Cagliari: ''Ku duba launina kenan''

Dan wasan kungiyar Pescara ta Italiya Sulley Muntari ya fice daga fili domin nuna bacin ransa kan katin gargadi da alkalin wasa ya ba shi bayan da ya yi korafin cewa ana masa cin mutuncin wariyar launin fata.

Tsohon dan wasan tsakiya na Ghana mai shekara 32 ya bukaci alkalin wasa Daniele Minelli ya dakatar da wasan na ranar Lahadi na gasar Serie A wanda suke yi a gidan Cagliari.

Amma sai alkalin wasan ya ba shi katin gargadi a minti na 89 bisa laifin kawo rudu a wasan, lamarin da ya harzuka tsohon dan wasan na Portsmouth da Sunderland ya fice daga fili cikin fushi, yana nuna wa magoya bayan Cagliari hannunsa yana cewa: ''Wannan ne launi na."

Kociyan Pescara Zdenek Zeman, wanda aka ci kungiyarsa 1-0, ya ce, dan wasan ya bukaci alkalin wasan da ya dau mataki a kai, amma sai ya ce shi bai gani ba bai kuma ji komai na cin mutuncin da danwasan ya yi korafi ba.

Kociyan ya ce Muntari ya yi dai dai amma da bai fice daga fili ba, domin za mu iya yin korafi amma ba mu da ikon yin hukuncin.

Muntari yana AC Milan lokacin da abokin wasansa a kungiyar Kevin-Prince Boateng ya fice daga fili saboda wakar warinyar launin fata da magoya bayan Pro Patria suka rika yi masa a watan Janairu na 2013.

Lamarin ya jawo korafi da nuna goyan bayan ga Boateng a shafukan sada zumunta a lokacin, har Fifa ma ta mara masa baya, amma ta ce bai dace ba da ya fice daga wasan.

Kungiyar Pescara ita ce ta karshen teburin Serie A kuma tuni ta riga ta fadi zuwa gasar rukuni na biyu na Italiya.