Pochettino: Nasara kan Arsenal ta bai wa Tottenham kwarin guiwa kan Chelsea

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Tottenham 2-0 Arsenal: Mauricio Pochettino ya ji dadin rawar da kungiyarsa ta taka

Nasarar Tottenham kan Arsenal na nufin za ta iya kara matsin lamba kan Chelsea a saman teburin gasar Firimiya, in ji kociya Mauricio Pochettino.

Kociyan dan asalin Argentina ya ce nasarar da kungiyarsa ta yi kan Arsenal da 2-0, "aba ce mai kayatarwa ga magoya bayanmu" yayin da Spurs ta tabbatar da cewar za ta kawo karshen jiran da ta yi na tsawon shekara 22 domin tsere wa abokiyar hamayyarta ta areawcin Landan, Arsenal.

Amman ya kara da cewar abu mafi muhimmanci shi ne kulob dinsa zai iya ci gaba da gogayya da jagorar gasar wadda ta doke Everton 3-0 ranar Lahadi.

Pochettino ya ce : "Muna cikin gasar, kuma gibin da ke tsakaninmu ya koma maki hudu."

"Dole mu mayar da hankali yanzu. Muna da wani babban wasa da West Ham ranar Juma'a. Wasa ne na gogayya da kawar hamayyar cikin gida.

"Wannan wasan zai iya kasance mana damar matsa wa Chelsea. Za mu riga su wasa, kuma in muka yi nasara, za mu ga abin da zai faru a lokacin da Chelsea za ta kara da Middlesbrough a filin Stamford Bridge ranar Litinin."

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Yadda Kungiyoyin kwallon kafa na gasar Firimiya na sama suke bayan wasannin da aka buga ranar Lahadi

Nasarar Chelsea a Everton daga farko a ranar Lahadi ta kara wa kungiyar maki inda ta kara tazarar da ke tsakaninta da babbar mai kalublanatarta a gasar, Tottenham da maki bakwai.

Amman kwallo ta 21 da Dele Alli ya ci wa kulob dinsa da kuma fenaretin da Harry Kane ya ci sun sama wa Tottenham nasara ta tara a jere a gasar Firimiya, lamarin da ya kara jerin nasarorin da kungiyar ta samu tun shekarar 1960, a lokacin da ta ci wasanni 13 a jere, kuma nasara ta rage ratar da ke tsakanin Chelsea da Tottenham zuwa maki hudu.

Kungiyar Chelsea ta kasance a saman teburi tun ranar biyar ga watan Nuwamba, kuma ta fi kungiyar da ke binta da maki 10 a ranar 19 ga watan Maris.

Amma daga baya an doke ta a wasanni biyu - a wasansu da Crystal Palace da kuma Manchester United.

"Na fahimci dadin da magoya bayanmu ke ji domin muna dab da gama gasar a saman Arsenal, amman bana jin irin wannan dadin saboda ni ina son in lashe kofin ne," in ji Pochettino.

"Muhimmin abu gare mu yanzu shi ne mu yi kokarin lashe gasar Firimiya a ko wacce kaka- abin da muke so kenan.

"Da gaske zai yi wuya, amman za mu ga abin da zai faru."

Wasan ranar Lahadi shi ne wasan karshe na abokan hamayyar cikin gida na arewacin Landan (Arsenal da Tottehma) da za a buga a White Hart Lane a halin da kungiyar ke ciki yanzu.

Tottenham za ta buga wasanninta na kaka mai zuwa ta 2017-18 a filin wasan Wembley yayin da ake gina sabon filin wasanta.

Ana gina sabon filin wasan ne mai daukar mutum 61,000 a gefen inda suke wasa yanzu.

Wasannin da suka rage wa Tottenham a kakar 2016-17
Juma'a, 5 ga watan Mayu West Ham (A waje)
Lahadi, 14 ga watan Mayu Man Utd (A gida)
Alhamis, 18 ga watan Mayu Leicester (A waje)
Lahadi, 21 ga watan Mayu Hull (A waje)
Wasannin da suka rage wa Chelsea a kakar 2016-17
Litinin, 8 ga watan Mayu Middlesbrough ( A gida)
Juma'a, 12 ga watan Mayu West Brom (A waje)
Litinin, 15 ga watan Mayu Watford (A gida)
Lahadi , 21 ga watan Mayu Sunderland (A gida)
Asabar, 27 ga watan Mayu Arsenal (Wasan karshe na gasar kofin kalubale)
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Tottenham 2-0 Arsenal: Tottenham ta cancanci nasara - Arsene Wenger

A shekarar 1995 ne kakar da Tottenham ta gama gasar Firimiya sama da Arsenal , a lokacin da suka kasance na bakwai kuma Gunners suka zama na 12.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba