Zlatan Ibrahimovic 'zai murmure ya dawo taka-leda'

Dan wasan Manchester United Zlatan Ibrahimovic Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ibrahimovic ya ji ciwo ne a lokacin wasan gasar Europa League da suka doke Andelecht

Wakilin Zlatan Ibrahimovic, Mino Raiola ya ce an yi nasara a tiyatar da aka yi wa dan wasan Manchester United din a cinyarsa kuma za ta koma daidai har ma ya koma buga kwallo.

Dan wasan mai shekara 35 ya ji ciwo a wasan gasar Europa League da suka doke Andelecht a ranar 20 ga watan Afrilu.

Sai dai Raiola ya jaddada a wata sanarwa cewa ciwon dan kasar ta Sweden ba abu ne da zai yi barazana ga aikinshi ba.

Ibrahimovic ya kusa kawo karshen kwantiraginsa a Old Trafford kuma bai yanke shawarar ko zai sabunta yarjejeniyarsa da kulob din ba.

Ya ci kwallo 28 a wannan kakar tun bayan dawowarsa United daga Paris St -German a karshen kakar da ta gabata.

Dan wasan na samun kulawa da horo a Pittsburgh inda aka yi masa tiyatar.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba