'Yar shekara 18 ta yi digiri a karatun lauya

Misis Joy Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Misis Joy ce mafi kankantaa da ta kammala karatun kauya

Wata matashiya haifaffiyar Najeriya ta zama mafi karantar shekaru da ta kammala karatun aikin lauya a Kwalejin Fourah Bay, ta Jami'ar Saliyo.

Joy Oluwagbemileke Jegede ta samu sakamako mai daraja ta daya a karatun digiri, tana 'yrn shekara 18, shekara daya bayan da ta samu digiri a fannin tafiyar da kasuwanci ta hanyar karatu daga nesa.

Iyayen Joy wadanda 'yan mishan ne, sun yi kaura zuwa Saliyo lokacin da take da shekara hudu.

An ba da belin tsohon gwamnan Niger Babangida Aliyu

Tana da shekara 13 ta rubuta jarrabawarta ta kammala sakandare.

A wata hira da ta yi da wakilin BBC, Umaru Fofana a birnin Freetown ta bayyana cewa, ''Abu ne da ya fara kamar wasa. Mahaifina na yi wa daliban da zasu rubuta jarabawar kamala karatun sakandire ta WASC bita, a karshen jawabin sai ya tambaye ni, ko za ki so ki rututa da su? Na yarda kuma na fara shiri domin cimma wannan buri.''

''A karshen jarabawar, na sami makin A guda uku da makin B guda hudu da kuma maki C daya,'' in ji Joy.

Ta kara da cewa, ''Domin cimma wannan buri iyayena sun taka muhimmiyar rawa. Mahaifiyata ta rika koya mini darasin Lissafi wato Maths yayin da mahaifina ya koya mini darasin Biology. Suka ta yi mini addua'a domin in samu ci gaba a rayuwata.''

Misis Joy ta kuma ce, "Yanzu ni ce karama a ajinmu kuma hakan abin alfahari ne."

Ta ce kamata ya yi dalibai su fahimci cewa, fahimtar darasin da ake koya maka ya fi samun sakamako mai kyau.

Labarai masu alaka