An tsare dan wasan Everton don kare 'lafiyar ƙwaƙwalwarsa'

Aaron Lennon Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Aaron Lennon ya yi wa Everton wasa shida a wannan kakar wasannin

'Yan sanda sun tsare dan wasan gefe na Everton Aaron Lennon, a karkashin tanede-tanaden da suka shafi dokar lafiyar kwakwalwa domin a kare lafiyarsa.

An dauki dan wasan mai shekara 30 zuwa asibiti domin a duba shi, bayan da aka kira 'yan sanda a birnin Salford ranar Lahadi.

"Yanzu dai Lennon na karbar kulawa da magunguna dangane da jinyar da ke da alaka da damuwa," in ji kungiyarsa.

Dan wasan mai bugawa Ingila wasa, ya koma Everton ne daga Tottenham a shekarar 2015, kuma bai buga wa kungiyar wasa ba tun watan Fabrairu.

Babban jami'in 'yan sandan birnin Manchester ya ce, "An kira 'yan sanda da misalin karfe 4:35 na yamma, lokacin da ciwon nasa ya tashi, a kan tsohon titin Eccles domin kula da lafiyarsa."

"Yan sanda sun je wajensa, kuma sun tsare shi karkashin sashi na 136 na tanede-tanaden da suka shafi dokar lafiyar kwakwalwa, kuma an kai shi asibiti domin kulawa da shi.

Labarin jinyar dan wasan dai ya ya ja hankalin magoya bayansa ma'abota shafukan sada zumunta da masu sha'awar wasanni, da kuma masu goyon bayan kungiyarsa ta yanzu da kuma kungiyar da ya baro.

Kungiyar Everton dai ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Laraba cewa: "Muna godiya da sakonninku dangane da dan wasan. Kuma muna goyon bayansa tare da ba shi kulawa sannan kuma iyalansa sun roki cewa a boye sirrinsa a wannan lokaci."

Labarai masu alaka