FA ta tuhumi Sunderland da Bournemouth

'yan wasan Sunderland da Bournemouth Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yan wasan sun yi ta ce-ce-ku-ce a filin wasa

Ana tuhumar kungiyoyin Sunderland da Bournemouth da laifin kasa shawo kan 'yan wasansu a wasan Premier na ranar Asabar a filin wasa na Stadium of Light.

Hukumar na tuhumar kungiyoyin a kan hatsaniyar da ta faru a minti na 76 lokacin da Bournemouth ta samu nasarar zura kwallo a raga, wanda hakan ya tabbatar da faduwar Sunderland daga gasar.

Hukumar ta FA ta ce kungiyoyin sun kasa shawo kan 'yan wasansu don su yi abin da ya dace.

An basu zuwa 5 ga watan Mayu domin amsa tuhumar.

'Yan wasan sun yi ta jayayya a tsakaninsu lokacin da dan wasan gaba na Sunderland Fabio Borini ya kalubalanci dan wasan baya na Bournemouth Lewis Cook.

Borini da dan wasan tsakiya na Bournemouth Harry Arter duk sun sami katin gargadi a wasan, saboda hatsaniyar.

Ita ma dai kungiyar Middlesbrough na fuskantar irin wannan tuhuma dangane da bugun daga kai sai mai tsaron gida, da aka ba ma Man City a minti na 66 a wasan da suka kara a filin wasa na Riverside ranar lahadi.

Labarai masu alaka