Za a ji ta bakin Moyes kan zargin barazanar marin 'yar jarida

David Moyes Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption David Moyes ya kasance kociyan Sunderland tun watan Yulin bara

Kociyan Sunderland, David Moyes, ya samu lokaci domin mayar da martani ga zargin da hukumar kwallon kafa ta Ingila ta yi masa na yin barazanar marin wakiliyar BBC, Vicki Sparks.

An tuhumi Moyes da laifin bata sunan wasan kwallon kafa da kalaman da ya yi bayan wasan kungiyarsa da Burnley a watan Maris.

Da farko dai an bashi zuwa ranar 3 ga watan Mayun Shekarar nan don ya mayar da martani ga zargin da ake masa, amman kocin mai shekara 54 ya nemi a kara masa lokaci.

Kocin dan asalin Scotland, yanzu ya samu lokaci zuwa ranar 10 ga watan Mayu.

Kalaman Moyes na zuwa ne bayan wata hirar da ya yi da Sparks inda ta tambaye shi kan ko kasancewar mai Sunderland, Ellis Short, a filin wasa ya kara masa matsi.

Sai Moyes ya ce "a'a'", amman bayan hirar sai ya shaida wa Sparks cewar, "Za ki iya shan mari duk da cewar ke mace ce," yana mai karawa da cewar ta mayar da hankalinta nan gaba.

A lokacin Sunderland na kokarin kaucewa faduwa daga rukunin gasar Firimiya zuwa rukunin gasar Zakarun Turai, amman faduwar kungiyar daga rukunin gasar Firimiya ya tabbata bayan kungiyar Bournemouth ta doke Sunderland a gida 0-1 a ranar Asabar..

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba