Nigeria: An harbe 'yan kunar bakin wake uku

Kunar Bakin wake Hakkin mallakar hoto .
Image caption Jami'ai sun kwashe gawarwakin 'yan kunar bakin waken

Ranotanni daga Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa an harbe 'yan kunar bakin wake uku a lokacin da suke neman afkawa sojoji.

'Yan kunar bakin waken uku wadanda suka nufi wurin gadin sojoji wanda ya ke kusa da Tashar Muna, an harbe su kafin su karasa wajen kuma bama-baman da suka daura a jikinsu sun tashi.

Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawan ta Najeriya (NEMA) a yankin arewa maso gabas, Ibrahim Abdulkadir, ya tabbatar da cewar hukumarsa ta dauke gawargwakin 'yan kunar bakin waken.

Ya kara da cewar jami'ai tsaron da ya ji rauni a fashewar bama-baman 'yan kunar bakin waken yana samun kulawa a yanzu haka.

Kungiyar Boko Haram dai tanaci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake a birnin na Maiduguri, tun bayan da jami'an sojin Najeriya suka ce sun fatattekesu daga dajin Sambisa da kuma garuruwan da suka kama a a yankin.

Sai dai masu sharhi na ganin a yanzu 'yan kungiyar ba su da karfin da za su kai wani gagarumin hari kamar yadda suke yi a baya, sai dai su dinga kai harin kunar bakin wake irin wannan.

Labarai masu alaka