Mourinho na 'sukar' kokarin da 'yan wasa ke yi — Sutton

Morinho Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mourinho dai ya soki kokarin da Luke Shaw, da Chris Smalling da kuma Phil Jones

Tsohon dan wasan gaba na Blackburn Chris Sutton ya ce kocin Manchester United, Jose Mourinho na "wulakanta 'yan wasa" ta hanyar sukar kokarinsu.

Sutton ya fada a wata hira da gidan Radiyon BBC cewa abin da Mourinho ke yi kasada ce da ka iya sa 'yan wasan su juya masa baya.

Ya kara da cewa, "Bai kyauta ba da ya ce ba sa wasa yadda ya dace."

Luke Shaw, dan wasan baya zai rasa sauran wasannin wannan kakar, saboda ciwon kafa da ya samu a wasan da suka tashi 1-1 da Swansea ranar Lahadi.

Shi dai Jones, wanda ke fama da ciwon yatsu, da kuma Smalling wanda ke fama da ciwon gwiwa, ba su yi wa kungiyar tasu wasa ba tun ranar 19 ga watan Maris, amma yanzu sun dawo don buga wasan da kungiyar za ta yi da Celta Vigo na gasar Europa ranar Alhamis.

Sutton ya kara da cewa "Manajojin da na yi wasa a karkashinsu za su gargadeka a dakin shiryawa, amma kuma su kan goyi bayanka a bainar jama'a. Amma Mourinho ba haka yake ba. Ina ganin wannan shi ke haifar da matsala".

Mourinho dai ya soki kokarin da Luke Shaw da Chris Smalling da kuma Phil Jones suke yi na dawo wa daga jinya.

"Fadin haka da ya yi, ni a ganina, yana gaya wa hukumar gudanarwar kungiyar, cewa ba ya bukatarsu a kungiyar, yana bukatar a musanya su. in ji Sutton

Labarai masu alaka