Ronald Koeman: kocin Everton na 'mafarkin' zama kocin Barcelona

Ronald Koeman
Bayanan hoto,

Ronald Koeman ya yi mataimakin kocin Barcelona tun shekarar 1998 zuwa 2000

Kocin Everton Ronald Koeman ya fada wa jaridar wasanni ta Catalan, cewa yana mafarkin zama kocin tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona,

Koeman, wanda tsohon dan wasan baya na Barcelona ne, a shekarun 1989 zuwa 1995, ya ce burinsa a yanzu shi ne kai Everton gasar Zakarun Turai.

Kocin mai shekara 54, na kakarsa ta farko cikin kwantiragin shekara uku da ya kulla da kungiyar daga Southampton a kakar da ta gabata.

An alakanta Koeman da komawa Nou Camp ne, bayan da Luis Enrique ya ce zai yi ritaya a karshen kakar wasa ta bana.

Kocin dan kasar Jamus ya ce, "Kaina yana fasuwa kuma ina jin cewa ba su manta da ni ba."

"Kowa ya san cewa ni dan Barcelona ne, sun san soyayyar da nake yi wa kungiyar, wacce na taso a cikinta har na zama wani abu."

"A rayuwata a matsayin Koci, akwai mafarki biyu da nake yi. Na farko, shi ne zama kocin kasata wato Holland. Ya kamata in yi wannan, amma babban buri na game da Everton ya kangeni daga wannan a yanzu. Mafarkina na biyu shi ne wata rana in zama kocin Barcelona, wannan shi ne gaskiya."

Everton dai na matsayi na bakwai a kan teburin Premier, yayin da ya rage wasa uku a kammala gasar, kuma kungiyar na dab da rasa gurbi a gasar ta Zakarun Turai a shekara mai zuwa.