Defoe zai bar Sunderland ni kuwa zama daram — Moyes

David Moyes and Defoe Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Moyes ya kulla kwantiragin shekara hudu da Sunderland

Kocin Sunderland David Moyes ya ce zai ci gaba da jan ragamar kungiyar duk kuwa da faduwa daga gasar Premier da kungiyar ta yi.

Kungiyar dai ta samu gagarumin koma baya a kakar bana, inda ta yi nasara sau biyar kadai a kakar ta bana, wanda hakan ya sa ta fadi daga gasar yayin da ya rage wasa hudu a kammala gasar.

Kocin dan Scotland ya ce dan wasan gaba na kungiyar Jermain Defoe, wanda ya ci kwallo 14 a wannan kakar, zai bar kungiyar.

A watan da ya gabata ne dai magoya bayan kungiyar suka yi ta kiraye-kirayen kocin ya bar kungiyar, tare da rera wakokin neman ya tafi lokacin da kungiyar ta yi rashin nasara a hannun Middlesbrough da 1-0.

Haka kuma yana fuskantar tuhuma daga hukumar FA, saboda ya ce wakiliyar BBC za ta sha mari.

Labarai masu alaka