Man City: Bravo ya gama wasa a kakar bana

Claudio Bravo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bravo ya ji raunin ne a wasan da kungiyar ta kara Man Utd

Mai tsaron ragar Manchester City Claudio Bravo ba zai buga sauran wasa hudun da suka rage wa kungiyarsa na kakar bana ba, saboda jinyar raunin da ya ji.

Dan wasan mai shekara 34, ya ji raunin ne a wasan da kungiyar ta tashi babu ci tsakaninta da abokiyar hamayyarta Man Utd.

Yanzu dai Willy Caballero ne zai karasa sauran wasannin kakar ta bana, yayin da kungiyar ke fatan kare gasar a mataki na hudu don samun gurbi a gasar Zakarun Turai mai zuwa.

Kocin kungiyar Pep Guardiola, ya tabbatar da cewa dan wasan gaba na kungiyar, Sergio Aguero ba zai buga wasan da kungiyar za ta kara da Crystal Palace ranar Asabar ba.

Dan wasan Argentinan ya samu rauni ne a karawar da kungiyar ta yi da Middlesbrough, amma zai dawo wasa a wasan gaba da kungiyar za ta yi.

Guardiola ya kara da cewa, "Aguero ba zai yi wasa ba. Amma muna fata zai buga wasan da za mu yi da Leicester."

Labarai masu alaka