Chapecoense ta dauki kofin farko bayan hadarin jirgin sama

'Yan wasan Chapecoense Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sabbin 'yan wasa 25 kungiyar ta Chapecoense ta Brazil ta dauka a bana

Kungiyar Chapecoense ta Brazil ta dauki kofinta na farko tun bayan da mafi yawan 'yan wasanta suka mutu a wani hadarin jirgin sama da ya faru a watan Nuwamba.

A karo na biyu a jere kungiyar ta dauki kofin Santa Catarina a ranar Lahadi duk da cewa abokiyar karawarta Avai ta doke ta da ci 1-0.

To amma kasancewar a wasan farko ita ce ta ci 1-0, wanda hakan ya sa ta fi yawan nasara a kakar wasannin bana, wannan ya ba ta damar daga kofin.

Kungiyar ta sadaukar da nasarar ga wadanda suka mutu a hadarin jirgin saman, inda sabon kociyansu Vagner Mancini ya ce, daman sun sani cewa za su gamu da matsaloli saboda yadda suke kokarin sake gina kungiyar.

Kociyan ya kara da cewa, to amma saboda aikin da suka dage suna yi su ka yi nasarar daukar kofin, inda suka rika doke abokan hamayyar da suke da wuyar ci.

A ranar 29 ga watan Nuwamba ne hadarin ya faru, yayin da 'yan wasan kungiyar ke kan hanyarsu ta zuwa karawa da Atletico Nacional a wasan karshe na cin kofin zakaru na Latin Amurka, Copa Sudamericana.

'Yan wasa uku ne kawai na kungiyar ta Brazil suka tsira a hadarin na watan Nuwamba, lokacin mutane 71 daga cikin 77 da ke cikin jirgin saman suka mutu.

Manyan kungiyoyi daga Brazil da Argentina suka yi musu tayin ba su aron 'yan wasa, inda a bana suka dauki sabbin 'yan wasa 25, kuma suka debo tara daga kungiyar matasansu.