Ina alfahari da 'yan wasana duk da rashin nasara - Mourinho

Jose Mourinho
Image caption Mourinho ya ce duk da Arsenal ta ci su burinsu na tunkarar wasansu da Celta Vigo ranar Alhamis cikin shiri ya cika

Kociyan Manchester United Jose Mourinho ya ce yana alfahari da 'yan wasansa tare da yaba musu duk da doke su 2-0 da Arsenal ta yi a Emirates, abin da ya kawo nakasu ga fatansu na zama cikin hudun farko a teburin Premier.

Kociyan ya ce ; ''Ba shakka mun san cewa ba mu shiga wasan ba da karfinmu sosai, to amma wannan shawara ce da aka yanke.''

Ya ce; '' Muna son mu ga mun dauki Kofin Europa ne wanda ya fi mana muhimmanci a kan mu samu matsayi na hudu a Premier.

Lalle muna son daukar kofin, domin mu samu damar zuwa gasar Kofin Zakarun Turai ta haka.

Saboda haka muna bukatar ba wa 'yan wasanmu hutu domin muna da karancin 'yan wasa.''

Mourinhon ya ce ta kai har akwai lokacin da 'yan wasansu biyar ne suke jinya, wadanda ba ta yadda za su warke su dawo su yi wani wasa a yanzu.

Kociyan ya ce, yana fata wannan dabara da suka yi za ta sa 'yan wasan nasu su kasance cikin shiri sosai domin wasan na ranar Alhamis.''

Domin su dai a wurinsu kamar yadda ya ce burinsu na ganin 'yan wasan sun tunkari karawar ta Alhamis cikin shiri ya cika.

Rashin nasarar na ranar Lahadi ya sa maki hudu ne yanzu tsakanin United a bayan abokiyar hamayyarta Manchester City wadda ke matsayi na hudu, kuma maki biyar tsakaninta da Liverpool ta uku, ko da yake United din tana da kwantan wasa daya.

Ko da Manchester United din ba ta gama gasar ta Premier a cikin hudun farko ba, za ta samu gurbin gasar cin Kofin Zakarun Turai, idan ta dauki kofin Europa.

United conclude their Europa League semi-final against Celta Viga at Old Trafford on Thursday, having beaten the Spanish side 1-0 in the first leg on Thursday.