Sabon shugaban Caf Ahmad ya ki karbar albashi

Shugaban Caf, Ahmad
Bayanan hoto,

Ahmad ya ce tsarin biyan albashin na yanzu na da alamun rashin gaskiya a cikinsa

Sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka Caf, Ahmad, wanda zabensa a watan Maris ya kawo karshen shugabancin Issa Hayatou na Kamaru na shekara 29, ya ce ya ki karbar albashi daga hukumar saboda babu alamun shugabanci na gari a tsarin.

Sabon shugaban ya ce wajibi ne tsarin albashin na dukkanin ma'aikata da na 'yan kwamitin zartarwa da kuma na shugaba ya kasance a bayyane.

Hukumar kwallon kafar ta Afirka CAF ta gudanar da taronta na gaggawa na farko karkashin jagorancin sabon shugaban, inda Mambobin hukumar ta CAF suke gudanar da taron a Bahrain, kafin babban taron Fifa, ranar Alhamis.

Akwai abubuwa da dama da sabon shugaban ke son a tattauna, da suka hada da abin da ya kira sabon tsari na tafiyar da hukumar a bisa tsari na gaskiya da amana (keke-da-keke).

Ahmad dan madagasacar mai shekara 57, wanda ke amfani da suna daya kawai, sauye sauye a hukumar shi ne abin da ya fi ba wa fifiko, ya ce kan haka ne ma a yanzu yaki karbar wani albashi daga hukumar kwallon kafar ta Afirka.

Haka kuma a yayin taron an zabi shugaban hukumar kwallon kafa ta Masar Hani Abo Rida, ya zama dan majalisar hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa.

Zaben nasa ya sa yanzu 'yan Afirka da ke cikin majalisar zartarwar hukumar kwallon kafar ta duniya, Fifa, wadda za ta yi babban taronta ranar Alhamis zuwa bakwai.

Sannan a yayin taron na Caf a ranar Litinin din nan an nada shugaban hukumar kwallon kafa ta Ghana Kwesi Nyatakyi, a matsayin mataimakin shugaban Caf din na farko.

Shi kuwa shugaban hukumar kwallon kafa ta Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo Constant Omari, ya samu mukamin mataimakin shugaban Caf din na biyu.

Mutanen biyu za su rinka wakiltar shugaban na Caf ( Ahmad) a duk lokacin da ba ya nan.

Haka kuma taron hukumar ya amince da sauyin kasafin kudin hukumar, domin ba wa shugaba Ahmad damar aiwatar da sabbin tsare-tsarensa.