Chelsea na dab da daukar kofi, Middlesbrough ta fadi

Diego Costa bayan ya ci kwallonsa ta 20 ta Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwallon Diego Costa ita ce ta 20 da ya ci a Premier bana

Chelsea na dab da daukar kofin Premier na bana bayan da ta doke bakinta Middlesbrough suka fadi daga gasar a karo na hudu, da ci 3-0, a Stamford Bridge.

Diego Costa ne ya fara daga raga a minti na 23 da shiga fili, kafin Alonso ya biyo baya da ta biyu a minti na 34.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci kuma ana minti na 65 sai Matic ya zura wa bakin kwallo ta uku, kuma ta karshe.

Yanzu maki uku ya rage wa jagorar ta Premier, wadda za ta bakunci West Brom ranar Juma'a ta dauki kofinta na gasar na Premier a tarihinta.

Da wannan nasara ta Chelsea da maki 84 a wasan na mako 36 ta kara ratar da ke tsakaninta da Tottenham mai maki 77 wadda ke binta a baya da maki bakwai kenan.

Ita kuwa Middlesbrough sakamakon ya sa ta bi layin Sunderland wajen ficewa daga gasar, inda ya kasance a karo na hudu kenan da take faduwa, yayin da ya rage wasa biyu a kammala gasar.