Inter Milan ba ta ce komai ba kan Conte

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pioli ya rike kungiyoyi 11 wadanda suka hada da Lazio, da Parma da Bologna

Inter Milan ta ki ta ce komai kan rade-radin da ke cewa tana shirin daukar kocin Chelsea Antonio Conte bayan ta dakatar da kocinta Stefano Pioli..

Rahotonni daga Italiya na cewa kungiyar na shirin daukar Conte kan kudi fam 250,000 duk mako, in dai ya bar Chelsea bayan kakar wasa daya.

An kori Pioli ne a ranar Talata bayan ya jagoranci kungiyar na wata shida.

Pioli mai shekara 51, ya maye gurbin Frank de Boer a watan Nuwamba, inda ya kulla kwantiragi da kungiyar har zuwa watan Yunin shekarar 2018.

Antonio Conte, mai shekara 47, ya taba jagorantar kungiyar Juventus daga shekarar 2011 zuwa 2014.

Inter Milan dai na matsayi na bakwai a kan teburin Serie A, yayin da ya rage wasa uku a kammala gasar, kuma ba ta samu nasara ba a wasa bakwai da ta buga.

Yanzu dai Kocin karamar kungiyar Stefano Vecchi ne zai karbi ragamar babbar kungiyar domin karasa kakar bana.

Pioli shi ne kocin Inter na tara tun bayan da Jose Mourinho ya bar kungiyar a shekarar 2010.

Labarai masu alaka