Fifa na bincike kan cinikin Pogba

Paul Pogba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pogba ya buga wa United wasa 48 a kakar wasa ta bana

Hukumar kwallon kafa ta duniya za ta binciki ciniki mafi tsada a duniya da Manchester United ta yi da Juventus, a kan sayen dan wasan tsakiya na kungiyar Paul Pogba, a shekarar da ta gabata.

Fifa ta rubuta wa kungiyar takarda tana neman Man U din ta yi mata cikakken bayani game da yarjejeniyar cinikin dan wasan.

Ana so ne dai a gano su waye ke da hannu a cinikin da ya kai na fam miliyan 89.3, kuma ta ya ya aka biya su kudin.

Mai magana da yawun Man U ya ce, "Ba ma magana a kan kwantiragin mutum daya. Ya kara da cewa hukumar na da bayanai game da cinikin tun lokacin da aka yi shi a watan Agusta."

Pogba, mai shekara 24, ya kara dawo wa Old Trafford ne, bayan da ya bar ta ya koma Juventus kan kudi fam miliyan 1.5 a shekarar 2012.

Dan wasan tsakiyar na Faransa, ya fara zuwa United ne daga kungiyar Le Havre ta Faransa a shekarar 2009.

Ya kara dawo wa United a kakar wasa ta bara a matsayin dan wasa mafi tsada a duniya a kan kudi fam miliyan 105.

Haka kuma United din ta amince ta biya Juventus karin kudi fam miliyan 4.5 idan dan wasan ya kara sanya hannu da kungiyar.

Labarai masu alaka