Nahiyar Afirka ta samu ƙarin gurabe a gasar kofin duniya

Gasar kofin duniya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Babu wata kasar Afirka da ta taba daukar kofin duniya a tarihinsa na shekara 87

Hukumar kwallon ƙafa ta duniya Fifa, ta amince da ƙara wa Afirka gurabe tara, a ƙoƙarin fadada ƙasashen da ke halartar gasar, zuwa kasashe 48, a gasar da za a yi a shekarar 2026.

An amince da wannan ƙuduri ne ranar Talata a ƙasar Bahrain. Nahiyar ta Afirka dai yanzu na da gurabe biyar ne a gasar.

Majalisar ta Fifa ta yi wani ƙuduri, wanda zai taimaka mata wajen raba wa nahiyoyin duniya, ƙarin guraben 48 ranar 30 ga watan Maris.

Ƙudurin fadadawar zai bai wa nahiyar Turai guraben tawaga 16.

A watan Janairu ne dai jami'an Fifa suka zabi da a ƙara fadada ƙasashen da ke halartar gasar daga ƙasashe 32 zuwa 48, daga shekarar 2026.

Guraben da aka bayar:

Asiya: gurabe 8 - ya karu daga kashi 4.5 (a yanzu tana da mambobi 46)

Africa: gurabe 9 - ya karu da biyar (a yanzu tana da mambobi 54)

Nahiyar Arewacin Amurka da kasar Amurka : gurabe 6 - ya karu daga kashi 3.5 (a yanzu tana da mambobi 34)

Nahiyar Kudancin Amurka : gurabe 6 - ya karu daga kashi 4.5 (a yanzu tana da mambobi 10)

Nahiyar Oceania: gurbi - ya karu daga kashi 0.5 (a yanzu tana da mambobi 11)

Turai: gurabe 16 - ya karu daga kashi 13 (a yanzu tana da mambobi 55)

Labarai masu alaka