Lauren: Wenger ya saba da matsin lamba

Wenger
Bayanan hoto,

Wenger na fatan samun gurbi a gasar Zakarun turai mai zuwa

Tsohon dan wasan baya na Arsenal ya ce matsin lamba ba zai sa Arsene Wenger ya yi murabus ba.

Arsenal din dai za ta kara da Southampton a gasar Premier a ranar Laraba, samun nasara a wasan dai zai kai kungiyar mataki na biyar a kan tebur.

Kocin dan kasar Faransa, wanda kwantiraginsa da kungiyar zai kare a karshen kakar wasa ta bana, ya fuskanci suka daga magoya bayan kungiyar.

Lauren,mai shekara 40 ya shaida wa BBC cewa "Ya saba jure matsin lamba, amma muna fata abubuwa za su koma daidai ko-ba-dade-ko-ba-jima".

Tsohon dan wasan baya na Kamarun ya ce "Ba na tunanin zai yi ritaya. Ya fuskanci matsin lamba na tsawon shekaru 30 zuwa 35, kuma ya rike manyan kungiyoyi, da matsin lamba mai yawa.

Lauren ya yi wa Arsenal wasa 159 tsakanin shekarar 2000 zuwa 2007 kuma yana cikin tawagar da ta dauki kofin kakar wasa ta 2003/2004.

A watan Fabarairu ne dai Wenger ya ce zai bayyana makomarsa, a watan Maris ko Afirilu game da sabunta kwantaragi da kungiyar, amma daga baya ya ce ya yi kuskuren sanya lokacin.