Mourinho ya ce ba su yi kasada ba kan fifita gasar Europa

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jose Mourinho ya ce ba zai yi nadama ba idan suka kasa zuwa gasar Zakarun Turai ta hanyar cin Kofin Europa

Kociyan Manchester United Jose Mourinho yana ganin bai yi wata kasada ba da ya ba wa gasar kofin Europa fifiko a kan samun gurbin hudu na gaba na Premier, yana mai cewa lissafi ne kawai.

Mourinho ya ce yanayin yawan wasan da suke yi ne ya sa dole su yi wannan zabi, wanda ake gani kamar kasada ce.

Ya ce: "Wasa 17 a cikin mako bakwai, abu ne da ba zai yuwu ba. Ba kasada ba ce, kawai yanayi ne da muka samu kanmu.''

Kociyan dan Portugal ya ce: "Shawara ce kawai da aka yanke bisa amfani da hankali da tunani."

A yanzu dai Manchester United ita ce ta biyar a teburin Premier, maki hudu tsakaninta da ta hudu Manchester City yayin da ya rage wasa uku a kammala gasar ta bana.

Mourinho ya yi sauyi takwas a cikin 'yan wasansa da yake sa wa na yau da kullum, a wasan da Arsenal ta doke su 2-0 ranar Lahadi, abin da ya kawo karshen wasanni 25 da ba a doke kungiyar ba.

Kociyan yana da kwarin guiwa cewa gasar Europa ce babbar damar da suke da ita ta samun zuwa gasar Zakarun Turai, kuma ya ce ba zai yi nadama ba idan ba su samu zuwa gasar ba.

United wadda ta ci Celta Vigo 1-0 a wasansu na farko a gidan kungiyar ta Spaniya, a yau Alhamis za ta karbi bakuncinta a Old Trafford.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wayne Rooney ya ci kwallo bakwai a wasa 38 a bana

Dan wasan gaba na Manchester United din Wayne Rooney ya goyi bayan kociyan nasu a kan wannan mataki da ya dauka na mayar da hankali kan gasar ta Europan.

Rooney ya ce: "Wannan kungiya ta gasar Zakarun Turai ce, kuma idan ka duba za ka ga abu ne mai wuya zuwanta gasar ta Zakarun Turai ta hanyar Premier, saboda haka dole ne mu mayar da hankali kan cin kofin na Europa.''