Japan: Amfani da tutar Nazi ya jawo wa kungiya fushin hukuma

Gamba a lokacin da take wasa Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Kungiyar ta Gamba ta haramta wa magoya bayanta shiga da tuta da kwalaye masu rubutu wasanninta

An ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Gamba Osaka ta kasar Japan tare da yi mata gargadi bayan da magoya bayanta suka daga wata tuta mai alama irin ta 'yan Nazi.

An ga wasu gungun magoya bayan nata ne sun daga tutar irin ta sojin Nazi, a lokacin da suke wasan gasar lig din kasar da abokan manyan abokan hamayyarsu Cerezo Osaka, a ranar 16 ga watan Afrilu.

Hukumar kula da gasar lig din kasar ta Japan ta ci kungiyar tarar fan 13,500 a kan laifin da magoya bayan nata suka yi.

Kungiyar ta haramta wa kungiyar wadannan magoya bayan duk wata mu'amulla da ita, har abada, sanna kuma har abada ta hana shiga duk wani wasanta da tuta da wani kwali ko wani abu mai wani rubutu da ake nunawa na wata manufa.

Gamba ita ce ta uku a teburin gasar ta Japan da maki 19 a wasa 10, kuma a ranar Lahadi ne za ta je gidan kungiyar Hokkaido Consadole Sapporo su kara.