Burina na dauki Premier a ranar Juma'ar nan - Conte

Antonio Conte Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Antonio Conte na bukatar nasara a wasa daya cikin uku da suka rage wa Chelsea ya dauki Premier a shekararsa ta farko

Yayin da Chelsea ke sa ran daukar Premier a Juma'ar nan, Antonio Conte ya ce ba abin da ya mayar da hankali a kansa yanzu kamar cimma wannan buri, kuma rahotannin da ke cewa zai koma Inter Milan ko alama ba sa dauke masa hankali.

Chelsea za ta dauki Premier a shekarar Conte ta farko a kungiyar idan ta yi nasarar bin West Brom gida ta doke ta a ranar Juma'a.

Ana dai rade radin cewa Inter Milan na harin tsohon kociyan na Juventus da tawagar kasar Italiya, bayan da kungiyar ta Serie A ta kori kociyanta Stefano Pioli ranar Talata bayan wata shida da kama aiki.

Sai dai Conte mai shekara 47 ya yi watsi da wannan rade radi yana mai cewa yana da sauran shekara biyu a kwantiraginsa da Chelsea kuma yanzu abin da ke gabansa da 'yan wasan da duk wani mai ruwa da tsaki a kungiyar shi ne daukar Premier.

A watan Afrilu ne 2016 aka sanar da nadin Conte a matsayin kociyan Chelsea, kuma ya fara kwantiragin shekara uku a watan Yuli da ya wuce bayan ya jagoranci tawagar kasar Italiya zuwa gasar cin Kofin kasashen Turai ta 2016.

Kociyan dan Italiya wanda sau uku a jere yana daukar kofin gasar Serie A ta Italiya da Juventus, kafin ya karbi aiki horar da tawagar Italiyan, ya farfado da Chelsea, wadda ta gama gasar a matsayi na 10 a kakar da ta wuce.

Inter wadda ke matsayi na bakwai a teburin Serie A ta ki cewa komai a kan rahotannin da ke cewa tana shirin zawarcin kociyan.

Kuma rahotannin na cewa kungiyar ta Serie A za ta yi kokarin shawo kan Conte da ba shi albashin fan 250,000 a duk mako idan ya amince ya bar Chelsea bayan kaka daya, ya koma wurinsu.