Everton ta ba wa Ross Barkley wa'adi

Ross Barkley Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Barkley ya ci kwallo hudu ya kuma bayar da takwas aka ci a wasa 34 da ya yi a Premier bana.

Kociyan Everton Ronald Koeman ya yi barazanar sayar da dan wasan kungiyar na tsakiya Ross Barkley in dai ban sanya hannu a sabon kwantiragi ba nan da mako mai zuwa, na karshen kakar bana.

A watan da ya wuce ne Koeman ya gargadi matashin dan wasan na tawagar Ingila, mai shekara 23, da cewa duk da shekara dayar da ta rage a kwantiraginsa za a iya sayar da shi.

A ranar Juma'ar nan Everton za ta kara da Watford kafin ta yi wasanta na karshe na Premier a gidan Arsenal ranar Lahadi 21 ga watan Mayu.

Kociyan dan Holland ya ce tsawon lokaci hukumar kungiyar ta Everton take ta kokarin ganin Barkley ya tsawaita kwnatiragin nasa amma bai yi ba, kuma tuni har ta fara neman wanda za ta maye gurbinsa da shi.

Koeman ya ce ba za su bari har zuwa watan Agusta ba, a karshen makon da ke tafe kawai suke son sanin matsayinsa.

Barkley ya ci kwallo hudu ya kuma bayar da takwas aka ci a wasa 34 da ya buga a Premier bana.