Giannelli: kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu

Giannelli Imbula Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption An fara wasa 23 da Giannelli a gasar Premier ta bana

Kocin Stoke City Mark Hughes, ya ce ɗan wasan ƙungiyar Giannelli Imbula na iya barin ƙungiyar a ƙarshen kakar wasa ta bana.

Dan wasan mai shekara 24 ya zo Stoke ne daga Porto a kan kuɗi fam miliyan 18.3. Sai dai kuma kocin ya ce ɗan wasan ya kasa taka rawar gani a ƙungiyar.

Dan wasan na Belgiyum mai shekaru 24, ya fara wasanni 23 ne kawai a gasar Premier ta bana, bayan da ya koma kungiyar daga Porto a kwantiragin shekara biyar da rabi da ya ƙulla a watan Fabrairu na 2016.

Kocin ya ƙara da cewa "Sau da dama abubuwa sukan zo maka yadda ba ka zato. Ba ya jin daɗin gasar Premier"

"Abin takaici ne ga kowannenmu. A gaskiya game da Giannelli abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata".

Imbula ya zama ɗan wasa mafi tsada da ya ƙulla kwantiragi a tarihin gasar kasar Portugal, lokacin da ya koma Porto daga Marseille a kan kuɗi Fam miliyan 15.1 a watan Yulin 2015.

Labarai masu alaka